Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Amir Abdallahiyan ya yaba game da kyakkyawan matsayin da kasashen rasha da china da kasashen turai 3 suka dauka kan tattaunawar da ake yi a vieanna na farfado da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma matsaya akai, tare da nuna bukatar Amurka ta yi amfani da hanyar da ta dace wajen tunkarar lamarin
Har ila yau y anuna fatansa na ganin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu iran da sabiya zata kara inganta da bunkasa musamman ta hanyar yin aiki tare na kafa kwamitin tattalin arziki a tsakaninsu
Ana sa bangaren ministan harkokin wajen kasar Sabiya ya sha alwashin cewa kasarsa za ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin ta kara fadada danagantakarta da kasar iran musamman a bangaren noma da kuma musayar dalibai.
342/